Rahotanni sun tabbatar da rasuwar Sadiq Gentle, wanda ke aiki a matsayin mai daukar rahoto ga Gwamnan Kano a Hukumar Kula da Tarihi da Al’adu, bayan da wasu ƴan daba suka kai masa mummunan hari a cikin dare.
Bayan harin, an garzaya da shi asibiti domin samun kulawar gaggawa, sakamakon raunukan da ya samu. Sai dai, duk da ƙoƙarin da likitoci suka yi wajen ceton rayuwarsa, ya riga mu gidan gaskiya.
Rahotanni sun bayyana cewa harin da aka kai masa ya jefa shi cikin mawuyacin hali kafin daga bisani ya rasu.