Gwamnatin tarayya ta bawa Ƙananun hukumomin arewa maso yamma Naira biliyan 537.1

0
12

Ƙananun hukumomin yankin Arewa maso Yamma sun karɓi fiye da naira biliyan 537.1 daga rarraba kudaden tarayya tsakanin watan Janairu zuwa Yuni 2025, bisa bayanan hukumomin kasa.

Jihohin su ne: Kano, Kaduna, Katsina, Jigawa, Sokoto, Kebbi, da Zamfara.

A cikin watannin shida, Kano ta fi sauran jihohi inda samu naira biliyan 130.4, yayin da Zamfara ta samu mafi ƙanƙanta da naira biliyan 44.

Adadin kudin da ake turawa yankin ya karu bayan watan Janairu, inda Fabrairu ya fi kowanne wata da naira biliyan 95.8, sai kuma Janairu da ya fi kankanta da naira biliyan 79.9. A matsakaita, yankin na karɓar kusan biliyan 89.5 a kowane wata.

Wannan rabo na nuna matsayin Kano na jiha mai yawan jama’a da muhimmanci ga tattalin arziki a Arewacin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here