Gwamnatin Kano Za Ta Tallafawa Iyalan ’Yan Wasan da Suka Rasu da Kuɗi da Filaye

0
14

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa za ta bai wa iyalan ’yan wasan da suka rasa rayukansu a wani mummunan haɗarin mota kuɗaɗe da kuma filaye a matsayin tallafi.

’Yan wasan guda 22, waɗanda dukkansu ’yan asalin jihar Kano ne, sun rasu ne a hanyar dawowa daga jihar Ogun bayan halartar  gasar wasanni ta ƙasa.

A cikin wata sanarwa da fadar gwamnatin jihar ta fitar ranar Laraba, an bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince a bai wa iyalin kowanne mamaci tallafin naira miliyan 11.7 da kuma fili.

Haka kuma, gwamnan ya bayyana cewa za a bai wa waɗanda suka tsira daga haɗarin naira miliyan 3.7 da kuma fili, a matsayin tausayawa da ƙarfafa guiwa.

Sanarwar ta ƙara da cewa tallafin ya haɗa da gudummawar da Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Remi Tinubu, da ɗan majalisa Sagir Koki, da gwamnatin jihar Ogun da kuma Hukumar Kwallon Volibol ta Ƙasa suka bayar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here