Tinubu ya taya murna ga ɗaliban Najeriya da suka samu nasara a gasar TeenEagle a London

0
8

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya wasu dalibai uku ‘yan Najeriya murna bisa lashe kambun zakarun duniya a gasar TeenEagle Global Finals 2025, wadda aka gudanar a birnin London, na ƙasar Birtaniya.

A cikin wata sanarwa da mai bawa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Laraba, Shugaba Tinubu ya yaba da wannan gagarumar nasara da daliban suka samu, yana mai bayyana su a matsayin madogarar hasken makomar Najeriya.

Daliban da suka samu wannan nasara su ne:

Nafisa Abdullahi Aminu (mai shekara 17)

Rukayya Muhammad Fema (mai shekara 15, da Hadiza Kashim Kalli, wanda suka wakilci Najeriya a gasar da ta tattaro dubban dalibai daga ƙasashe 69, kuma suka samu nasara.

Sanarwar ta ƙara da cewa Shugaban ƙasa ya yaba da rawar da makarantu ke takawa wajen tarbiyya da horar da hazikan dalibai, yana mai bayyana nasarar a matsayin hujja da ke nuna ingancin tsarin ilimi a Najeriya.

Tinubu ya kuma bukaci Nafisa, Rukayya da Hadiza da su ci gaba da dagewa a karatunsu tare da fatan samun ƙarin nasarori a rayuwarsu.

Daliban na karatu a Nigerian Tulip International College da ke Jihar Yobe, inda gwamnatin jihar da wasu sanannun ‘yan Najeriya suka riga suka yaba da nasararsu.

Daga cikin waɗanda suka yaba da nasarar har da Shugaban Jami’ar Maryam Abacha American University da tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, wanda a wani saƙo da ya wallafa a shafin Facebook ya bukaci gwamnatin tarayya da ta bawa daliban lambar yabo ta ƙasa. Ya kuma kwatanta nasararsu da ta ƙungiyoyin kwallon kafa na mata (Super Falcons) da D’Tigress, wanda Tinubu, ya basu kudade da yaba musu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here