Soja ya halaka ɗan sanda da wuka a jihar Taraba

0
10

Wani mummunan al’amari ya faru a birnin Jalingo, na jihar Taraba, inda aka zargi wani soja mai suna Dauda Dedan, ya daɓa wa wani jami’in dan sanda,  Aaron John, wuka in ya mutu har lahira.

Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 9 na daren ranar Litinin a unguwar Mayo-Goyi, kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, James Lashen, ya tabbatar wa da manema labarai a ranar Laraba.

A cewar sa, John ya amsa kiran gaggawa daga mazauna yankin da suka koka kan wata hayaniya da ake zargin sojan ne ya haddasa, amma da isarsa wurin, sai rikicin ya rikide zuwa tashin hankali, inda aka ce sojan ya daba masa wuka har ya mutu.

Bayan faruwar lamarin, sojan ya tsere daga wajen. Sai dai rundunar soji ta bayyana cewa ta fara bincike tare da tabbatar wa da ‘yan sanda cewa suna kokarin kama Dedan. Dukkanin hukumomin tsaron sun ce za su yi aiki tare domin tabbatar da adalci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here