Rashin kudi ne ya hana Tinubu naɗa Jakadu—Sanata Jimoh

0
11

Sanata Jimoh Ibrahim, mai wakiltar Ondo ta Kudu, ya bayyana cewa jinkirin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu wajen naɗa sabbin jakadu ya samo asali ne daga matsanancin hali na tattalin arziƙi.

A watan Satumban 2023 ne shugaban ƙasa Tinubu ya bayar da umarnin a janye dukkan jakadu na kwararru da wadanda ba kwararru ba daga ƙasashen da suke wakilta.

Tun daga lokacin har zuwa yanzu, ba a sake naɗa sababbin jakadu ba.

Sanata Jimoh ya ce Najeriya tana cikin mawuyacin halin kuɗi a lokacin da wannan gwamnati ta hau mulki, kuma naɗa jakadu na buƙatar kuɗaɗe masu yawa.

Ya ƙara da cewa shugaban ƙasa na fuskantar manyan matsaloli da dama, kuma yana buƙatar lokaci kafin ɗaukar muhimman matakai.

“Na tabbatar shugaban ƙasa zai naɗa sabbin jakadu nan ba da jimawa ba. Naɗa jakadu na buƙatar kuɗi, kuma lokacin da wannan gwamnati ta hau, Najeriya tana cikin mummunan halin kuɗi,” in ji shi.

“Akwai matsaloli da dama a gaban shugaban ƙasa, dole ne ya fara da abubuwan da suka fi muhimmanci.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here