Mafi yawancin ƴan siyasar Najeriya basu da tarbiyya–Sarkin Kano Sunusi

0
11

Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana cewa babban dalilin da ke janyo yawaitar cin hanci da rashawa a Najeriya shi ne rashin tarbiyya tun daga tushe, musamman a tsakanin ‘yan siyasa da masu rike da madafun iko.

A wata hira da aka yi da shi a cikin shirin Politics Today na Channels TV a daren Laraba, Sanusi ya ce yawancin masu mukaman gwamnati sun hau kujerar ne ba bisa kwarewa ko kishin kasa ba, sai dai don wata manufa ta kansu.

“Da yawa daga cikin masu rike da mukamai ba su da tarbiyyar gaskiya da rikon amana,” in ji shi. “Yawanci sun shiga gwamnati ne saboda dalilai na son zuciya.”

Sarkin ya ce halayen kirki da darajar da al’umma ke mutunta su sun dusashe gaba ɗaya. Ya ce: “Yanzu marasa tarbiyya ne ke mulkar kasar; mutane da ba su da abin alfahari kuma ba su da niyyar barin wani abin kwatance bayan sun tafi.”

Sanusi ya kuma bayyana damuwarsa kan yadda mutane ke fifita dukiya da jin daɗi fiye da mutunci da nagarta.

“Mutane suna alfahari da dukiyar da suka tara, irin su gidaje da jiragen sama, amma ba sa tunanin yadda al’umma ke kallon su a matsayin ɓarayi,” in ji shi.

Ya kara da cewa matsalar ba ta tsaya ga shugabanni kadai ba, hatta sarakuna da malamai da ke jan ragamar jagoranci sun fada cikin ruɗani.

“Ko shugabannin addini sun ruɗe, haka ma sarakuna. Kusan kowa ya fada tarkon wannan ruɗanin,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here