Kwamishinan harkokin sufuri na Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Ali Namadi, ya ajiye mukaminsa sa’o’i kadan bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi rahoton kwamitin bincike da aka kafa domin duba rawar da Kwamishinan ya taka a batun bayar da beli ga wanda ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Alhaji Namadi ya bayyana cewa ya yanke shawarar sauka daga mukaminsa ne saboda samun kwanciyar hankalin al’umma da kuma la’akari da mahimmancin al’amarin.
A cewarsa: “A matsayina na mamba a cikin gwamnati da ke fafutukar yakar shan miyagun ƙwayoyi da fataucin su, dole na ɗauki wannan mataki duk da cewa ya yi tsauri. Ko da yake ina nan kan bakana cewa ni ba ni da laifi, amma ba zan iya watsi da yadda jama’a ke kallon al’amarin ba, musamman domin kare nagartattun manufofin da muka gina.”
Alhaji Namadi ya nuna godiya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa damar da ya bashi na yi wa jihar hidima.
Ya ƙara da cewa: “A matsayina na ɗan ƙasa nagari, wajibi ne na kare amana da hangen nesan da muka dasa a jihar Kano. Har ila yau, ina nan daram da manufofin da suka kawo wannan gwamnati.”
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi murabus ɗin cikin girmamawa tare da yi masa fatan alheri a rayuwarsa ta gaba.
Haka kuma, Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci rashin da’a ko halayen da ke da nasaba da laifukan miyagun ƙwayoyi da sauran munanan dabi’u da ke shafar matasa da al’umma baki ɗaya ba.
A ƙarshe, Gwamnan ya gargadi dukkan masu rike da muƙaman siyasa da su rika taka-tsantsan a duk wani lamari da ya shafi jama’a, tare da neman izini daga hukumomi masu iko kafin ɗaukar kowace irin matsaya.