Gwamnatin Tarayya ta bayyana hasashen ruwan sama mai yawa da ake sa ran zai ɗauki tsawon kwanaki biyar daga 5 zuwa 9 ga watan Agusta, 2025, wanda zai iya haddasa ambaliya a jihohi 19 da kuma gurare 76 a faɗin ƙasar nan.
Wannan gargaɗi ya fito a ranar Talata daga Cibiyar Gargaɗin Ambaliya ta Ƙasa (National Flood Early Warning Systems Centre) ƙarƙashin Ma’aikatar Muhalli ta Ƙasa, inda aka bukaci hukumomi da mazauna yankunan da abin zai shafa da su ɗauki matakan gaggawa don kauce wa asara.
Wannan na zuwa bayan ambaliya mai tsanani ta afkawa wasu sassan jihohin Ogun da Gombe a ranar Talata, yayin da wasu jihohin kamar su Legas, Filato, Anambra da Delta suma suka fuskanci irin hakan.
Rahoton hasashen ambaliyar da cibiyar ta fitar ya bayyana cewa ana sa ran ruwan saman zai shafi wurare da dama kamar haka,
Akwa Ibom: Edor, Eket, Ikom, Oron, Upenekang
Bauchi: Tafawa-Balewa, Azare, Jama’are, Kari, Misau, Jama’a
Ebonyi: Abakaliki, Echara, Ezilo
Cross River: Ogoja Edor, Obubra
Nasarawa: Keana, Keffi, Wamba
Benue: Agaku, Buruku, Gboko, Igumale, Ito, Katsina-Ala, Ugba, Vande-Ikya
Kaduna: Jaji, Kafancha, Birnin-Gwari, Zaria
Katsina: Bindawa, Bakori, Daura, Funtua
Kebbi: Bagudo, Birnin-Kebbi, Bunza, Gwandu, Jega, Kalgo, Kamba, Kangiwa, Shanga, Ribah, Sakaba, Saminaka, Yelwa, Gauri-Banza
Kano: Bebeji, Gezawa, Gwarzo, Birnin Kano, Karaye, Tundun-wada, Wudil, Kunchi
Niger: Kontagora, Rijau, Ringim
Plateau: Mangu
Taraba: Donga, Takum
Jigawa: Diginsa, Gumel, Dutse, Gwaram, Hadejia, Miga
Yobe: Machina, Potiskum
Zamfara: Anka
Sokoto: Sokoto, Wamakko
Borno: Biu
Gombe: Bajoga
Ana shawarci jama’a da su kiyaye, su bi hanyoyin bayar da agajin gaggawa, kuma su kasance cikin shiri domin kare rayuka da dukiyoyin su daga haɗarin ambaliya.