Gwamnatin tarayya ta kulla yarjejeniya da Asusun Cigaban Tattalin Arzikin Larabawa na ƙasar Kuwait, domin samun rance mai rangwame na dala miliyan 25.35, domin aiwatar da shirin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Jihar Kaduna.
Wannan rance na daga cikin hadin gwiwar kudade da suka kai jimillar dala miliyan 62.8 da aka tanada tare da hadin gwiwar abokan ci gaba na kasa da kasa, don fadada damar samun ilimi mai inganci a yankin da ke daga cikin mafiya fama da matsalar rashin shiga makaranta a Najeriya.
Cikin wata sanarwa da daraktan sashin hulɗa da jama’a na ma’aikatar kudi ta tarayya, Mohammed Manga, ya fitar a ranar Talata, an bayyana cewa kudaden za su taimaka wajen aiwatar da shirin kai ilimi ga yaran da ba sa zuwa makaranta, wanda ke mai da hankali kan yara masu rauni kamar ‘yan mata, yara masu nakasa da kuma wadanda rikice-rikice suka raba da muhallansu.
Ana sa ran shirin zai bai wa fiye da yara 100,000 damar shiga makaranta, ginawa da gyara fiye da makarantu 200, da kuma inganta yanayin koyarwa da horar da malamai a yankunan da ke fama da rashin isasshen kayan more rayuwa.
Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya tabbatar da cewa ilimi na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ke bai wa muhimmanci, inda ya bayyana cewa jihar ta riga ta biya na ta kaso na dala miliyan 1 a matsayin kudin da aka nema daga wajen ta don aiwatar da shirin.