Gwamnatin jihar Kaduna ta amince da bayar da hutun watanni shida ga dukkan ma’aikatan gwamnati mata da suka haihu, domin karfafa shayar da jarirai nono kadai cikin watanni na farkon rayuwarsu.
Mataimakiyar Gwamnan jihar, Dr. Hadiza Balarabe, ce ta bayyana hakan a ranar Litinin yayin wani taron bikin Makon Shayar Da Jarirai Nonon Uwa na Duniya na 2025 da aka gudanar a Kaduna.
Taron ya samu halartar kungiyoyin raya ci gaban al’umma, wakilan ƙungiyoyin fararen hula, da kuma jami’an hukumar UNICEF.
Ta bayyana cewa shayar da jarirai nono kadai yana rage yawan kamuwa da cututtukan yara, yana rage kudaden kula da lafiya, tare da inganta kwakwalwa da kwarewar tunani a wajen jarirai.
A nasa jawabin, Kwamishinar Lafiya ta jihar Kaduna, Umma Ahmed, ta bayyana cewa ma’aikatar ta bude dakin kula da jarirai a hedikwatarta domin tallafawa matan da ke shayar da jarirai.