Jami’an rundunar tsaron a’lumma ta farin kaya Civil Defence, NSCDC a Jihar Kano sun kama wasu maza biyu da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi da shiga gidajen mutane don yi musu sata.
Mai magana da yawun rundunar, Ibrahim Abdullahi, ya ce an kama Basiru Ahmed, mai shekara 42, a Salanta dake ƙaramar hukumar Gwale, dauke da buhunan tabar wiwi fiye da guda 100, kuma an mika shi ga hukumar NDLEA don bincike da daukar mataki.
Haka kuma, an kama wani matashi mai suna Muhammad Abbas, dan shekara 22, a Gurungawa dake Kumbotso, bisa zargin shiga gidaje yana aikata sata.
Abdullahi ya ce za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike, sannan ya bukaci jama’a su ci gaba da bai wa hukumomi hadin kai wajen yaki da aikata laifuka.