Zagin malamai ba abun alkairi bane—Uba Sani

0
5

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya gargadi ’yan siyasa da masu amfani da kafafen sada zumunta da su daina cin mutuncin malamai, yana mai cewa hakan yana barazana ga zaman lafiya da hadin kan al’umma.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin ganawarsa da shugabannin addini da na gargajiya a birnin Kaduna, inda ya jaddada muhimmancin rawar da malamai ke takawa wajen wanzar da zaman lafiya.

“Idan muka bari a rika zagin malamai ba tare da wani dalili ba, to mu sani cewa hakan zai iya lalata tsaron ƙasa da zaman lafiyar al’umma. A koda yaushe idan abubuwa suka tabarbare, malamai muke komawa wajen neman addu’o’i da shawarwari,” in ji Gwamnan.

Malam Uba Sani ya nuna damuwa kan yadda wasu ‘yan siyasa ke haɗa kai da mutane marasa kishin kasa wajen ɓata suna da yin kage ga malamai a kafafen sada zumunta.

Ya kuma shawarci shugabanni da magoya bayansu da su guji amfani da malamai domin cimma manufofin siyasa ko wata buƙata ta kai-da-kai. A cewarsa, hakan na iya haifar da rudani da rashin jituwa a tsakanin al’umma, ba kawai a Kaduna ba, har da Najeriya gaba ɗaya.

Gwamna Uba Sani ya yaba da irin goyon bayan da malamai ke ba gwamnatinsa tun lokacin da ya hau karagar mulki. Ya bayyana su a matsayin ginshiƙan wanzar da zaman lafiya da haɗin kai a jihar.

Sai dai kuma, ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda wasu ’yan siyasa ke watsi da malamai bayan sun cimma nasara a zaɓe, amma su koma nemansu da zarar an kusa yin wani zaɓen.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here