‘Yan Bindiga Sun Sace Mutane 26 a Zamfara

0
9

Yan bindiga sun sace mutane 26 a karamar hukumar Zurmi da ke jihar Zamfara.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru kasa da awanni 24 bayan wani gungun ‘yan bindiga dauke da makamai suka kai farmaki a ƙauyuka 16 da ke karamar hukumar Kaura Namoda, inda suka kashe mutane biyar tare da yin garkuwa da wasu da dama.

An kai hare-haren Kaura Namoda ne tsakanin ranar Asabar da Lahadi, inda ‘yan bindigar suka kuma sace dabbobi da dama da kudinsu ya kai miliyoyin naira.

Majiyoyi daga yankin sun ce ‘yan bindigar sun afka garuruwan Zurmi, da suka haɗar da, Dada da Gidan Shaho, inda suka sace mutum 24 tare da jikkata mutum daya.

An ce harin ya gudana ba tare da harbi ba, kuma ya ɗauki kusan awa ɗaya kafin ‘yan bindigar su fice daga yankin.

Da aka tuntubi Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Zamfara, CP Ibrahim Maikaba ta wayar salula, ya yi alƙawarin zai kira wakilin Daily trust, amma har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton bai kira ba domin jin ta bakin sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here