Shugaban ’yan ta’adda da ake zargi da ta’azzarar ayyukan ta’addanci a Jihar Zamfara, Bello Turji, ya saki mutum 32 da yayi garkuwa dasu tare da amincewa da dakatar da hare-hare a kan manoma, bayan ganawa da wasu malamai a maboyarsa.
Malam Musa Yusuf, wanda aka fi sani da Asadus-Sunnah, shine ya bayyana hakan a wani taron addini da aka gudanar a ranar Litinin a Kaduna.
Malam Yusuf ya ce Turji ya mika wasu daga cikin makaman da ke hannunsa bayan taron da aka gudanar a yankin karamar hukumar Shinkafi a Zamfara.
Ya ce al’ummar Shinkafi ne suka roki tawagar malamai su je su roki Turji ya ba su damar komawa gonakinsu da ke cikin dazuka. Ya bayyana cewa an yi taron ne sau uku a watan Yuli a dajin Fakai.
“A lokacin da muka gana da su Bello Turji, Dan Bakkolo, Black, Kanawa da Malam Ila, mun tabbatar cewa rade-radin da ake yadawa cewa Dan Bakkolo ya mutu ba gaskiya ba ne. Wadannan su ne ke addabar yankin, kuma dukkansu sun amince da shirin zaman lafiya, ciki har da mika wasu daga cikin makaman da ke hannunsu domin nuna cewa sun yarda da shirin.”
Malam Yusuf ya ce a cikin yarjejeniyar zaman lafiyar, Turji ya saki fursunoni 32 da ya yi garkuwa da su, inda ya nuna bidiyon wasu daga cikin mutanen da aka sako da kuma wahalhalun da suka fuskanta wajen zuwa sansanin Turji.
Ya kara da cewa wadanda aka sako sun hada da mata da yara, kuma sun shafe kusan watanni hudu a hannun ’yan bindigar. Wasu daga cikin matan da ke tsare sun haihu a cikin daji, yayin da daya daga cikinsu ta samu cizon maciji.