Sojojin sun hallaka mayaƙan Boko Haram 17 a Borno da Adamawa

0
7
Sojoji
Sojoji

Sojojin da ke karkashin rundunar Operation Hadin Kai a yankin Arewa maso Gabas sun hallaka mayaƙan Boko Haram 17 a wani samame da suka kai a jihohin Borno da Adamawa.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da mukaddashin darakta na sashen hulɗa da jama’a na rundunar, Kyaptin Reuben Kovangiya, ya fitar, inda ya bayyana cewa mayakan sun dade suna addabar al’umma a yankunan Bama, Konduga, Gwoza, Magumeri da Biu na jihar Borno, da kuma Michika a jihar Adamawa.

Sanarwar ta ce sojojin sun kuma kwance abubuwan fashewa fiye da 14 da ‘yan ta’addan suka dasa a wurare daban-daban, domin kai farmaki ga fararen hula da jami’an tsaro.

Haka zalika, a cewar sanarwar, sojojin sun kuma taimaka wajen dawo da fiye da ‘yan gudun hijira 987 zuwa garuruwansu na asali, musamman a Mandaragau da ke karamar hukumar Biu, jihar Borno.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here