Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya karɓi rahoton kwamitin bincike da aka kafa domin gano rawar da Kwamishinan Sufuri, Alhaji Ibrahim Namadi Dala, ya taka wajen bayar da beli ga wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi mai suna Sulaiman Aminu Danwawu.
Sanarwar hakan ta fito ne daga kakakin Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, a yau Talata.
Rahoton dai ya samu gabatarwa ta hannun Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, a wani taron musamman da aka gudanar a fadar gwamnatin Kano. A wajen taron, Sakataren ya bayyana mahimman abubuwan da kwamitin ya gano bayan zurfin bincike da tattara shaidun da suka dace.
Muhimman Abubuwan da Rahoton Kwamitin Bincike Ya Bayyana:
🔹 Bada Belin da Gangan: Kwamishinan ya miƙa buƙatar zama wanda zai tsaya beli ga wanda ake zargi a ranar 18 ga Yuli, 2025.
🔹 Shaidar Riko: Ya shaida a cikin rantsuwar sa cewa shi kwamishina ne kuma zai kiyaye dukkan sharuddan beli har zuwa ƙarshen shari’ar.
🔹 Sanin Sharuddan Beli: Ya san cewa sai wanda ke cikin majalisar zartarwa ta jiha da ke rike da mukamin gwamnati ne kawai zai iya zama mai tsayawa a bayar da belin bisa umarnin kotu.
🔹 Rashin Bincike Mai Zurfi: Kwamishinan bai nuna kulawa da bincike mai zurfi kafin ya yanke shawarar tsaya wa wanda ake zargi ba – duk da cewa ana tuhumarsa da laifin kwayoyi.
🔹 Sanin Nau’in Laifin: Kwamitin ya gano cewa Kwamishinan ya san da gaske irin laifin da ake tuhumar wanda ya tsayawa.
🔹 Sabanin Manufofin Gwamnati: Duk da sanin cewa gwamnatin jihar Kano ba ta yarda da safarar miyagun kwayoyi da sauran miyagun dabi’u ba, Kwamishinan ya yanke shawarar tsayawa mai neman belin.
🔹 Babu Alaka a Baya: Binciken ya nuna babu wata alaka ta baya tsakanin Kwamishinan da wanda ake zargin.
🔹 Babu Ribar Kuɗi Ko Sauran Fa’ida: Kwamitin bai samu wata shaida da ke nuna cewa an ba shi wani kuɗi ko wani abu ba.
🔹 Babu Kuɗin Beli da Kwamishinan Ya Biya: Binciken ya tabbatar cewa Kwamishinan bai biya ko sisin kobo na Naira miliyan 5 da ake dangantawa da belin.
Gwamna Yusuf ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da gaskiya, adalci da da’a a cikin harkokin gwamnati. Ya kuma bayyana kudurinsa na ci gaba da yaƙi da miyagun kwayoyi da duk wata dabi’a da ke lalata rayuwar matasa da al’umma baki ɗaya a Kano.