Matashiya ta shirya yadda aka sace ta don samun kuɗin fansa daga mahaifinta

0
10

Rundunar ƴan sandan Abuja ta kama mutum huɗu da suka haɗa da wasu mata biyu da samari biyu kan zargin shirya garkuwar ƙarya da nufin karɓar kuɗi daga mahaifiyar wadda aka sace.

Wani mutum mai suna Innocent ya kai ƙara cewa ƴarsa mai shekara 16 ta ɓace bayan ta tafi rubuta jarabawa. Daga bisani wasu suka kira shi da bukatar ya biya fansa naira miliyan biyar.

Binciken ƴan sanda ya gano cewa babbar yar uwar yarinyar tare da saurayinta ne suka shirya garkuwar tare da haɗin kan yarinyar. An same ta a wani gida tana cin abinci cikin natsuwa, ba tare da wata damuwa ba.

Dukkan waɗanda ake zargi sun amsa laifi, kuma ana shirin gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here