Shuwagabannin APC a jihar Kano sun bayyana cikakken goyon bayansu ga shirin sake tsayawa takara ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben shekarar 2027.
Haka kuma sun jaddada biyayyarsu ga jagoran jam’iyyar a jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Wannan goyon baya ya fito ne daga wani taron jiga-jigan jam’iyyar da aka gudanar a ranar Talata a gidan Dr. Ganduje da ke Kano. Taron ya mayar da hankali kan haɗin kai a cikin gida, shirin tunkarar zabe, da kuma bayyana ci gaban da gwamnatin Shugaba Tinubu ke aiwatarwa, musamman a Arewacin Najeriya.
Shugaban jam’iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas, wanda ya jagoranci taron, ya bayyana cewa an shirya taron ne domin ƙarfafa haɗin kai, warware sabani, da kuma sake tsara jam’iyyar don tunkarar babban zaben 2027.
Ya kuma bayyana cewa APC a shirye take ta karɓi ‘yan siyasa daga jam’iyyun adawa, musamman daga ƙungiyar Kwankwasiyya, idan suka yanke shawarar dawowa cikin jam’iyyar. Sai dai ya ja hankalin cewa APC ba za ta yi kasa a gwiwa wajen fuskantar adawa a filin siyasa ba idan har suka ƙi dawowa.
An tattauna kan ayyukan da gwamnatin tarayya ke gudanarwa a yankin, inda jiga-jigan jam’iyyar suka karyata zarge-zargen wariya ga yankin Arewa.
Cikin manyan jami’an jam’iyyar da suka halarci taron akwai:
Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, tsohon É—an takarar gwamna na APC a Kano,
Dr. Mariya Mahmoud Bunkure, Ministar Birnin Tarayya mai Karamar Hukuma,
Sanata Kawu Sumaila,
Hon. Alhassan Ado Doguwa,
Hon. Abubakar Kabir Bichi,
Hon. Sani Bala Tsanyawa, da wasu manyan masu rike da mukaman gwamnati da na jam’iyya daga matakai daban-daban.
Jiga-jigan jam’iyyar sun ɗauki alwashin ƙara himma wajen wayar da kan al’umma da gudanar da tsare-tsaren yaƙin neman zaɓe tun daga tushe domin tabbatar da nasarar jam’iyyar APC a matakin jiha da ƙasa baki ɗaya a shekarar 2027.