An samu gagarumar rashin nasara a jarrabawar WAEC ta 2025

0
6

Masana harkar ilimi da iyaye sun nuna damuwa matuƙa kan rashin kyakkyawan sakamako da dalibai suka samu a jarrabawar (WASSCE) da Hukumar Shirya Jarrabawa ta Afirka ta Yamma (WAEC) ta gudanar.

Sakamakon da aka fitar jiya Juma’a ya nuna cewa daga cikin ɗalibai 1,969,313 da suka zauna jarrabawar, ɗalibai 754,545 ne kawai wanda ke wakiltar kashi 38.32 cikin 100 suka samu ƙima (credit) a darussa biyar, ciki har da Turanci da Lissafi.

Shugaban ofishin hukumar WAEC na Najeriya, Amos Dangut, shi ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar hukumar da ke Legas. Ya ce wannan sakamakon na bana ya nuna koma baya da kashi 33.8 cikin 100 idan aka kwatanta da sakamakon shekarar 2024 da ya kai kashi 72.12 cikin 100.

Bincike ya nuna cewa wannan ne sakamako mafi muni tun daga shekarar 2020. A waccan shekarar, WAEC ta bayyana cewa ɗalibai 1,003,668 wato kashi 65.24 cikin 100 daga cikin 1,601,047 da suka zauna jarrabawar sun samu nasara a darussa biyar, ciki har da Turanci da Lissafi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here