Mazauna, matafiya da ‘yan kasuwa a birnin Lagos sun fuskanci matsanancin rashin jin dadi a ranar Litinin, sakamakon ambaliya da ta biyo bayan ruwan sama mai ƙarfi da aka fara samu tun daren Lahadi kuma ya ci gaba da sauka har zuwa Litinin.
Ruwan saman, wanda ya fara sauka kusan ƙarfe goma na dare, ya haddasa ambaliya a sassa daban-daban na Lagos lamarin da ya dakile harkokin kasuwanci da tattalin arziki.
Wasu mazauna birnin sun yi amfani da kafafen sada zumunta don neman taimako, inda suka yada hotuna da bidiyo na gidaje, motoci da tituna da ambaliya ta mamaye.
Bidiyon da suka karade shafukan sada zumunta sun nuna yadda ambaliya ta mamaye manyan yankuna kamar Ijede da ke Ikorodu, inda mazauna ke yawo cikin ruwa ko kuma sun makale a gidajensu.
A martaninsa kan wannan ambaliya, Kwamishinan Muhalli da Albarkatun Ruwa na jihar Lagos, Tokunbo Wahab, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta san da halin da ake ciki, kuma tana aiki kan wani shiri domin magance matsalar.