Ƴar Najeriya ta lashe gasar iya Turanci ta duniya a London

0
12

Wata ɗaliba ƴar shekara 17 daga jihar Yobe, Nafisa Abdullahi, ta kafa tarihi a gasar ƙasa da ƙasa ta harshen Turanci ta ‘TeenEagle’ da aka gudanar a Landan, babban birnin Ingila, inda ta lashe babban kambin gasar na shekarar 2025.

Nafisa ta doke sama da mahalarta 20,000 daga ƙasashe 69, inda ta fito zakara ta farko a matakin ƙarshe na gasar da aka fi sani da ‘UK Global Finals’. Wannan nasara ta nuna bajintar da ta yi a fagen iya amfani da harshen Turanci fiye da takwarorinta daga sassa daban-daban na duniya.

Wannan nasara da Nafisa ta samu ya sanya ta zama abin alfahari ga al’ummar Najeriya, musamman a jiharta ta asali wato Yobe.

An bayyana cewa Nafisa ta wakilci Najeriya ne karkashin makarantar Tulip International College (NTIC) da ke jihar Yobe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here