Ƴan bindiga sun kai hari a kauyen Sabon Garin Damri da ke ƙaramar hukumar Bakura a jihar Zamfara, inda suka sace mutane 60 ciki har da yara da mata, sannan suka kashe wani manomi a kauyen Rogoji da ke makwabtaka da yankin.
Wani mazaunin yankin, Isa Sani, ya bayyana cewa maharan sun shigo akan babura a ranar Asabar, inda suka bude wuta tare da yin garkuwa da jama’a. Ya ce har yanzu babu wani saƙo daga wurin masu garkuwar dangane da mutanen da suka sace.
Har ila yau, lamarin na zuwa ne kasa da mako guda bayan bayyanar wani bidiyo da ke nuna daruruwan mutane da ake zargin an sace su a Zamfara, a cikin wani daji.
A watan da ya gabata, an samu rahoton yadda ƴan bindiga suka yanka mutum 38 daga cikin 50 da suka sace a ƙauyen Banga, bayan karɓar kuɗin fansa.