WAEC ta saki sakamakon jarabawar 2025

0
8

Hukumar Shirya Jarabawa Kammala Makarantun Sakandire ta Ƙasashen Yammacin Afirka (WAEC) ta sanar da sakin sakamakon jarrabawar wannan shekara.

Bayanin hakan na kunshe cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Litinin, 4 ga watan Agusta, 2025.

Hukumar ta bayyana cewa dukkan ɗaliban da suka zauna jarabawar yanzu za su iya duba sakamakonsu ta yanar gizo.

An shawarci ɗaliban da su shiga shafin duba sakamako na hukumar a http://waecdirect.org tare da amfani da bayanan jarabawarsu da lambobin binciken sakamako (result checker pins) domin duba sakamakonsu.

A wani bangare na sanarwar, shugaban ofishin WAEC na Najeriya, Amos Dangut, ya bayyana cewa an samu raguwa da kashi 33.8 cikin ɗari a yawan ɗaliban da suka samu nasara a sakamakon bana idan aka kwatanta da na shekarar 2024.

Yayin da yake zantawa da manema labarai a Legas, Dangut ya ce an samu koma baya wajen yawan ɗaliban da suka samu sakamakon (credit) a darussa biyar, ciki har da Turanci da Lissafi.

A cewar hukumar, ɗalibai 1,973,253 daga makarantu 23,554 da aka amince da su ne suka zauna jarabawar ta bana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here