Tsofaffin Sojoji Sun Yi Zanga-Zanga a Abuja Akan Haƙƙokinsu

0
11

Wasu tsofaffin sojojin Najeriya da suka yi ritaya sun gudanar da zanga-zangar lumana a Abuja, inda suka bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta biyan su haƙƙokinsu da suka dade ana jira.

Zanga-zangar ta gudana ne a ranar Litinin a gaban harabar Ma’aikatar Kuɗi ta Ƙasa, inda tsofaffin sojojin da suka yi murabus da bisa ra’ayin kansu daga aikin soja a ranar 1 ga Yuli, 2024, suka hallara domin bayyana ƙorafinsu.

Daga cikin bukatunsu akwai, cikakken biyan kudin ritaya (gratuities), alawus bisa sabon albashin ƙasa, kuɗin da suka saka a tsarin gidaje, kudin NAWIS/BenFund, da sauran su.

Masu zanga-zangar sun nuna ɓacin ransu kan jinkirin da aka samu wajen biyan haƙƙokinsu, suna masu bayyana hakan a matsayin rashin daraja da nuna halin ko-in-kula da gudunmawar da suka bawa ƙasa. Sun jaddada cewa tunda sun cika nasu nauyin, wajibi ne gwamnati ta cika nata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here