Rahotanni daga wasu kafafen yaɗa labarai a makon da ya gabata sun ruwaito cewa shugaban kamfanin man fetur na ƙasa (NNPC), Bayo Bashir Ojulari, ya yi murabus daga muƙaminsa. Sai dai sabon bayani da jaridar Vanguard ta samu daga wata majiya mai tushe ya bayyana cewa labarin ba gaskiya ba ne.
Wata majiyar tsaro ta ce Ojulari ya bayyana a ofis dinsa da misalin ƙarfe 9:35 na safiyar Litinin, inda ya ci gaba da gudanar da aikinsa kamar yadda aka saba, lamarin da ke nuni da cewa ba wani murabus da yayi.
A cewar majiyar, an fitar da wata sanarwa ta cikin gida ga ma’aikatan NNPC, inda aka bukaci su yi watsi da duk wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta kan batun murabus ɗin.
A ƙarshen mako, rahotanni sun yi zargin cewa jami’an tsaron DSS da na EFCC sun tilasta wa Ojulari rubuta takardar murabus. Sai dai har yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga NNPC ko gwamnatin tarayya da ke tabbatar da hakan.
A wani hoto da ya bayyana a safiyar Litinin, an ga Ojulari yana halartar wani taron ƙungiyar injiniyoyin harkar man fetur ta manhajar Zoom, wanda ke gudana a Legas.
A tun ranar 2 ga watan Afrilu, 2025, ne shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Bayo Bashir Ojulari a matsayin shugaban NNPC, domin ya maye gurbin Mele Kyari.