Ruwan sama mai ƙarfi da iska da aka tafka a ranar Lahadi ya yi barna a wasu yankuna na jihohin Filato da Bauchi, inda ya rusa gidaje da gonaki tare da raba ɗaruruwan mazauna jihohin da muhallansu.
A ƙauyen Menkaat da ke gundumar Shimankar a ƙaramar hukumar Shendam ta jihar Filato, rahotanni sun nuna cewa sama da gidaje 50 sun rushe, ciki har da makarantu da cibiyar ibada.
Haka kuma, a ƙaramar hukumar Dass ta jihar Bauchi, akalla iyalai fiye da 40 ne suka rasa matsugunansu, yayin da ruwan sama ya tafi da amfanin gonaki da dama.
A jihar Neja ma, ambaliya ta mamaye gonaki da dama a wasu yankuna, musamman a ƙauyen Kafin Koro da ke cikin ƙaramar hukumar Paikoro, sakamakon ruwan sama da aka tafka tun safe.
Rahotanni sun kuma nuna cewa ambaliyar ta shafi al’ummomi 18 a ƙaramar hukumar Lapai, inda aka samu lalacewar gonaki, tare da barazanar rugujewar wasu karin gonaki da ke kan gaba.