Gwamnatin tarayya zata hana shigo da Madara daga ƙasashen waje

0
10

Ma’aikatar cigaban harkokin Kiwo ta Tarayya tare da Kamfanin Cigaban Sabuwar Najeriya (NNDC) sun bayyana aniyar su na hada gwiwa domin rage yawan kudin da Najeriya ke kashewa wajen shigo da madara daga waje, wanda kuɗin ya kai sama da dala biliyan 1.5 a duk shekara.

Wannan kuduri ya biyo bayan wani babban taro da aka gudanar a ranar Juma’a a hedikwatar ma’aikatar da ke Abuja, inda bangarorin biyu suka tattauna akan tsarin hadin gwiwa a karkashin shirin dabarar hanzarta bunkasa harkar kiwon dabbobi a kasa baki daya.

A yayin taron, Ministan cigaban harkokin Kiwo, Alhaji Idi Mukhtar Maiha, ya bayyana cewa wannan hadin gwiwar na da damar sauya akalar harkar samar da madara a Najeriya.

Ya kara da cewa ma’aikatar na da cikakken shiri na kirkirar manyan hanyoyin kiwo masu dorewa, tare da tallafi daga kwararru, ingantattun kayan aiki, da kuma samar da dama ga makiyaya da kuma masu kiwo na zamani domin amfanin kowa da kowa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here