Gwamnatin Kano Ta Karɓi Rahoton Bincike Kan Kwamishinan Harkokin Sufuri

0
13

Kwamitin da Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kafa domin bincikar zarge-zargen da ake yi wa Kwamishinan Harkokin Sufuri, Hon. Ibrahim Ali Namadi, dangane da belin Danwawu da ake zargin aikata Safarar miyagun ƙwayoyi ya kammala aikinsa tare da mika rahoton binciken ga gwamnatin jihar.

Kwamitin, ƙarƙashin jagorancin Barrister Aminu Hussaini, ya mika cikakken rahotonsa ga Sakataren Gwamnatin Jiha a ranar Litinin. Binciken ya mayar da hankali kan zargin cewa kwamishinan ya taimaka wajen bayar da beli ga wani da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi.

A cikin aikinsa, kwamitin ya ce ya tattauna da masu ruwa da tsaki, ya nazarci muhimman takardu, ya yi hira da shaidu, tare da duba tsarin doka da aka bi wajen bayar da belin.

Kwamitin ya bayyana cewa burin binciken shi ne tabbatar da adalci da kuma tabbatar da cewa duk wata matsaya da gwamnati za ta ɗauka tana bisa hujjoji masu ƙarfi da tsarin doka.

Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada aniyarta ta mutunta doka da gaskiya, tare da bayyana cewa ba za a kare kowanne jami’in gwamnati ba idan aka same shi da laifi.

An fara binciken ne bayan zargin cewa Kwamishina Namadi ya nemi zama mai tsayawa ga wani da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu, a gaban Kotun Tarayya da ke Kano. 

Bisa bayanan kotu, mai shari’ar ya gindaya sharuddan beli masu tsauri da suka haɗa da sai kwamishina mai ci ya tsaya masa jingina, inda Namadi ya amince da hakan a farko, amma daga baya ya janye saboda matsin lamba daga jama’a.

Bugu da ƙari, wata majiya daga Hukumar Tsaro ta SSS ta bayyana a cikin rahoton sirri cewa Namadi ya karɓi $30,000 daga hannun Danwawu a matsayin cin hanci domin ya tsaya masa jingina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here