Yan arewa su kyale Tinubu ya kammala abinda ya fara—Fadar shugaban ƙasa

0
56

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ya bukaci tsoffin ‘yan majalisar arewacin Najeriya da su goyi bayan shugaba Bola Tinubu a yunkurinsa na sake neman wa’adin mulki a 2027.

Gbajabiamila ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin wani taron tattaunawa na ‘yan arewa da kungiyar tsoffin ‘yan majalisar arewa, da aka gudanar a birnin Abuja.

Femi Gbajabiamila, ya jaddada muhimmancin hadin kan ‘yan siyasa daga arewa wajen goyon bayan shugaba Tinubu, yana mai bayyana shi a matsayin jagoran da ya nuna kwarewa da sadaukarwa wajen hada kan kasa.

“A matsayinsa na shugaban kasa, Tinubu ba dan kudu bane kaɗai, sai dai jagora na kasa baki daya wanda ya bai wa kowane yanki muhimmanci,” in ji Gbajabiamila.

Ya kuma jaddada ayyukan raya kasa da gwamnati ke aiwatarwa a arewa, ciki har da gina sabbin hanyoyi, fadada layin dogo da bunkasa harkar noma, a matsayin shaida na adalcin gwamnatin Tinubu.

“Daga manyan ayyukan more rayuwa har zuwa gyare-gyaren dokoki, yankin arewa na cin gajiyar  wannan gwamnati mai gaskiya da rikon amana,” in ji shi.

“Yanzu muna gina tubalin ci gaba, kuma abu ne mai kyau a bar shugaban kasa ya kammala abin da ya fara.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here