Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ce Najeriya na fuskantar babban kalubale da koma baya idan har APC ta sake lashe zaɓen shekarar 2027.
El-Rufai ya bayyana haka ne a ranar Asabar yayin wani taron yaɗa manufofin gamayyar jam’iyyun adawa a ƙarƙashin ADC wanda aka gudanar a jihar Sokoto.
Ya ce ya shiga gamayyar ne da nufin ganin an sauke jam’iyyar APC daga mulki.
Tsohon jigon jam’iyyar APC ya bayyana cewa yana da niyyar haɗa kai da ’yan Najeriya domin kawar da jam’iyyar da ya kira mai “rashin iya mulki.”
“Ina siyasa ba don tara kuɗi ba, sai don hidimtawa jama’a,” in ji shi. “Idan gwamnati ba ta sauke nauyin da ke kanta ba, to ya zama wajibi a gare ni a matsayin dattijon kasa, in fito in nuna rashin jin daɗi tare da ɗaukar matakin gyara.”