Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya tabbatar wa da mazauna Maiduguri cewa babu wani haɗari game da yawaitar ruwa a Dam ɗin Alau, duk da ruwan sama da ake samu mai ƙarfi a kwanan nan.
Zulum ya bayyana hakan ne bayan yaje duba aikin gyaran dam ɗin, yana mai cewa kwararrun injiniyoyi sun tabbatar da cewa matakin yawan ruwan ya fara raguwa, kuma an bude sabbin hanyoyin wucewar ruwa don rage tasirin sa da yawan sa.
Ya gargadi jama’a da su guji gina gidaje a hanyoyin ruwa da kuma toshe magudanan ruwa, yana mai cewa hakan yana haddasa ambaliya. Ya bukace su da su kasance masu tsaftace magudanan ruwa a kowane lokaci.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar za ta sake duba tsarin gine-ginen birnin Maiduguri domin magance matsalolin da ke kara haddasa ambaliya. Ya ce tilasta bin dokokin muhalli zai zama dole, ko da kuwa ba zai yiwa wasu daɗi ba.