Rundunar tsaron a’lumma ta farin kaya reshen jihar Bauchi ta kama wasu mutum biyu tare da kwato wata mota ɗauke da kayan gine-ginen hanyar jirgin ƙasa da aka lalata, a ƙaramar hukumar Tafawa Balewa da ke jihar.
Mai magana da yawun rundunar, Saminu Yusuf, ne ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar a Bauchi, ranar Lahadi.
A cewarsa, jami’an NSCDC sun kama waɗanda ake zargin ne a ranar Talata, bayan samun sahihan bayanan sirri.
Ya bayyana cewa an kama motar haya kirar Peugeot J5 mai lamba KTG 40 XF, dauke da shinge-shinge 80 da aka cire daga hanyar jirgin ƙasa da kuma buhuna huɗu na gawayi.
Ya ƙara jaddada kudurin rundunar na kare dukkan muhimman kayayyakin gwamnati da ke da alaƙa da ci gaban ƙasa, tare da gargaɗin masu aikata laifin lalata kayan gwamnati da cewa doka ba za ta yi kasa a guiwa wajen hukunta su ba.
Ya kuma bukaci jama’a da su kasance masu sanya ido tare da bayar da bayanai cikin lokaci ga hukumomin tsaro domin dakile ayyukan masu tayar da hankali da barna.