Wasu matan aure daga unguwar Kofar Mata a garin Kano sun gudanar da zanga-zanga domin nuna damuwarsu kan yawaitar farmaki da kisan da ƴan daba ke aikatawa a yankin.

Matan sun bayyana cewa ƴan daban sun addabi unguwar da hare-hare da kuma kisan kai, inda suka ce a daren jiya wani matashi daga Jihar Katsina ya rasa ransa a hannun ƴan dabar.

Matan sun ce za su ci gaba da zaman dirshen a wajen har sai gwamnati ta dauki matakin da ya dace tare da halartar wurin domin jin ƙorafinsu da kawo mafita.
