NDLEA zata yiwa ɗalibai 800,000 gwajin shan miyagun ƙwayoyi

0
13

NDLEA zata yiwa ɗalibai 800,000 gwajin shan miyagun ƙwayoyi

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) tare da Ma’aikatar Ilimi sun kafa wani kwamiti domin tsara yadda za a aiwatar da gwajin ta’ammali da miyagun kwayoyi na dole ga ɗaliban manyan makarantu a faɗin Najeriya.

Wani babban jami’in NDLEA da ya tattauna da jaridar Punch, ya tabbatar da cewa tuni aka kammala shirye-shiryen fara aiwatar da shirin a farkon sabon zangon karatu mai zuwa.

Duk da cewa tsarin karatun manyan makarantu yana bambanta, wasu daga cikinsu za su fara sabon zangon karatu a watan Satumba.

Bisa bayanan Hukumar JAMB, akalla ɗalibai 800,000 ne aka ba su gurbin karatu a wannan shekarar. Rahoton baya-bayan nan na shekarun karatu hudu da suka gabata ya nuna cewa a kowace shekara, a kalla ɗalibai 800,000 ne ke samun gurbin shiga manyan makarantu irinsu jami’o’i, kwalejojin ilimi da kwalejojin fasaha (polytechnic).

A shekarar karatu ta 2023/2024 kadai ne adadin ya haura zuwa ɗalibai 900,000.

A wata sanarwa da mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar, Marwa ya bayyana amfani da kwayoyi a matsayin barazana ga tsaron ƙasa da cigaban matasa, yana danganta hakan da ta’addanci da ayyukan ‘yan bindiga.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here