Hukumar gudanarwar Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina ta amince da korar dalibai 57 saboda samun su da laifin aikata laifin satar amsa a lokacin rubuta jarabawa.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’ar ta fitar a ranar Asabar, wadda Hajiya Fatima Sanda, shugabar sashen yaɗa labarai da hulɗa da jama’a ta jami’ar, ta sanya wa hannu.
Sanarwar ta bayyana cewa hukuncin ya biyo bayan shawarwari da Kwamitin Nazarin Laifukan Magudi a Jarabawa na jami’ar ya bayar, a yayin taron majalisar jami’ar na 125.
An bayyana cewa kafin yanke hukuncin, kwamitin ya gudanar da bincike a sassa daban-daban na jami’ar domin tabbatar da gaskiyar laifukan.
Haka kuma, sanarwar ta ƙara da cewa an dakatar da wasu dalibai guda biyar daga karatu na tsawon zangon karatu biyu (shekarar 2024/2025), tare da soke takardun jarabawarsu.
Sannan wasu dalibai biyu kuma sun samu takardar gargadi, wadda za ta kasance cikin kundin tarihin karatunsu na har abada.
Jami’ar UMYU ta jaddada cewa wannan mataki na daga cikin tsauraran dokokinta na rashin yarda da aikata magudi a jarabawa, kuma anyi hakan domin zama izina ga sauran dalibai.
Sanarwar ta kuma jaddada cewa jami’ar na da niyyar kiyaye darajar ilimi da tsaftar jarabawarta, kuma ba za ta yi ƙasa a gwiwa wajen ɗaukar mataki kan duk wanda aka samu da laifi ba.