Gwamnan Kano ya bayar da kyautar motoci ga Civil Defence

0
7

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya mika kyautar wasu sabbin motoci na aiki ga rundunar tsaron farin kaya (NSCDC), domin tallafa musu wajen tabbatar da tsaro a fadin jihar.

An gudanar da bikin mika motocin ne a fadar gwamnatin Kano da ke Kwankwasiyya City, a wani bangare na shirin gwamnatin jihar na bai wa hukumomin tsaro kayan aiki na zamani domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Motocin da aka bai wa rundunar sun hada da na sintiri, taimakon gaggawa da kuma na leÆ™en asiri, wanda ana sa ran za su taimaka matuka wajen inganta ayyukan jami’an rundunar wajen fuskantar kalubalen tsaro a Kano.

Yayin bikin, Kwamishinan tsaro na jihar Kano ya bayyana cewa wannan tallafi ya nuna cikakken kudirin gwamnatin Abba Kabir Yusuf na samar da dukkan kayan aiki da goyon baya ga hukumomin tsaro.

A nasa jawabin, kwamandan NSCDC na jihar Kano ya gode wa Gwamna Yusuf bisa wannan gagarumar gudunmawa, yana mai cewa motocin za su taka muhimmiyar rawa wajen kara inganta sintiri da kare al’ummomin jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here