Ba na ɗaukar kaina a matsayin ‘yar Najeriya—Kemi Badenoch

0
12

Fitacciyar yar siyasar jam’iyyar Conservative ta Birtaniya, Kemi Badenoch, ta bayyana cewa ba ta ɗaukar kanta a matsayin ‘yar Najeriya, duk da cewa asalin danginta da kuma ƙuruciyarta ta yi su ƙasar.

Da ake zantawa da ita a wani shiri na tafka muhawara mai suna Rosebud podcast, tare da Gyles Brandreth, Badenoch ta ce tun sama da shekaru ashirin da suka wuce ba ta sabunta fasfo ɗinta na Najeriya ba, alamar nisanta kanta da ƙasar da ta shafe wani ɓangare na ƙuruciyarta.

An haifi Badenoch a birnin London a shekarar 1980, sannan ta dawo Birtaniya tana da shekaru 16 bayan shafe mafi yawan ƙuruciyarta a Najeriya da Amurka. Ta bayyana cewa duk da tana girmama asalin danginta na Najeriya, yanzu ta gina ainihin muhallinta ne bisa tarbiyya da rayuwarta a ƙasar Birtaniya.

A cewarta, “Gida” yana nufin inda mijinta, ‘ya’yanta da danginta na kusa ke zaune. Ta ƙara da cewa jam’iyyar Conservative ita ce ‘yar uwarta ta siyasa, tana nuna alaƙarta ta siyasa da ta zuciya da jam’iyyar.

Badenoch na daga cikin mutanen ƙarshe da suka amfana da tsarin bayar da haƙƙin zama ɗan ƙasa ta hanyar haihuwa a Birtaniya kafin a sauya dokar a shekarar 1981, lamarin da ya ƙara ƙarfafa kasancewarta yar Birtaniya a hukumance da a zahiri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here