Rundunar Sojin Ruwa ta bayyana shirinta na kafa sabuwar shalkwata a garin Yauri da ke Jihar Kebbi, domin ƙarfafa tsaro a hanyoyin ruwa da dakile laifuka a Kogin Niger.
Wannan bayanin hakan ya fito ne yayin wata ziyarar ban girma da tawagar sojin ruwa ƙarƙashin Rear Admiral Patrick Nwatu ta kai wa Gwamnan jihar Nasir Idris.
Nwatu ya ce Kogin Niger na kara zama hanyar safarar makamai da miyagun kaya, shi ya sa suka yanke shawarar zuwa Kebbi.
Gwamna Idris ya yaba da shirin, yana mai cewa kafa sansanin rundunar a Yauri ya dace da wannan lokaci, musamman duba da kalubalen tsaro da ke shafar yankunan da ke iyaka da Nijar da Benin. Ya kuma tabbatar da cikakken goyon bayan gwamnatinsa ga aikin.