Tinubu Zai Fara Karɓar Sabon Haraji Akan Man Fetur Da Dizal

0
17

Yayin da ’yan Najeriya ke fama da hauhawar farashin kaya, rashin tabbas a tattalin arziki da kuma tsananin rayuwa, ƙudurin gwamnatin tarayya na ƙara harajin kashi 5 cikin 100 (5%) kan man fetur da dizil, na cikin gida da wanda ake shigo da su, da zai fara aiki daga 1 ga Janairu, 2026, ya jawo ce-ce-ku-ce.

Tun bayan cire tallafin man fetur da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi a ranar 29 ga Mayu, 2023, da kuma faduwar darajar naira, hauhawar farashin kayayyaki ya ƙara tsananta, inda rayuwar talaka ta shiga hali na ƙunci.

Farashin abinci da sufuri ya ƙaru matuka, sannan hauhawar farashi ya shafi dukkan fannoni, daga magunguna da kuɗin makaranta, zuwa sadarwa da kudin wutar lantarki.

Ga al’ummar da ke fuskantar matsin tattalin arziki, ƙarin kuɗin haraji a kan man fetur da dizil ba zai zama abu mai sauƙi ba, sai dai ƙara wa jama’a ƙunci.

Daga watan Mayu 2023 zuwa yanzu, farashin man fetur ya ninka fiye da sau biyar, yayin da darajar naira ta fadi da fiye da kaso 60 cikin 100 idan aka kwatanta da dala. A ranar 31 ga Yuli, 2025, lita ɗaya na fetur na kai matsakaicin farashin naira 900, sabanin naira 187 da ake siya kafin Tinubu ya hau mulki.

Sabon harajin nan da za a fara a 2026 zai ƙara tsananta halin da gidaje ke ciki, inda kudaden da ake kashewa wajen rayuwa tuni suka wuce tunani sakamakon tsadar mai da dizil, wanda ke tasiri ga komai daga farashin kayan masarufi har zuwa kuɗin mota.

Saboda haka, masu ruwa da tsaki na ganin dacewar a cire wannan ƙarin haraji daga sabuwar dokar haraji domin kauce wa jefa ‘yan Najeriya cikin wani sabon mawuyacin hali, kamar yadda jaridar Punch, ta bayyana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here