Shugaban ƙasa Tinubu ya sauke Gawuna daga muƙamin sa

0
19

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sauke Dr. Nasiru Yusuf Gawuna daga mukaminsa na shugaban kwamitin gudanarwar Jami’ar Bayero da ke Kano.

 Shugaban ya nada AVM Saddik Kaita (mai ritaya) a matsayin wanda zai maye gurbinsa.

Sai dai sanarwar da fadar shugaban ƙasa ta fitar ta bayyana cewa Dr. Gawuna zai cigaba da rike mukaminsa na shugaban kwamitin gudanarwar Bankin bayar da lamunin gidaje wato (Federal Mortgage Bank of Nigeria).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here