Ma’aikatan jinya sun musanta janye yajin aikin da suke yi

0
8

Ƙungiyar Ma’aikatan Jinya da Unguwane ta Najeriya (NANNM) ta bayyana cewa yajin aikin da ta fara a faɗin ƙasa na ci gaba, duk da sanarwar da Ministan Lafiya Farfesa Ali Pate, ya bayar cewa an dakatar da shi.

Ministan ya bayyana hakan ne bayan wata ganawa da yayi da shugabannin ƙungiyar a Abuja a yau Juma’a, inda ya ce an cimma matsaya da shugabannin ƙungiyar don janye yajin aikin.

Sai dai shugaban ƙungiyar na ƙasa Morakinyo Rilwan, ya karyata wannan ikirari, inda ya ce babu gaskiya a maganar dakatar da yajin aikin.

“Idan Minista ne ya fara yajin aikin, to yana da ikon dakatar da shi. Amma tunda ƙungiyarmu ce ta shirya yajin aikin, to har yanzu yana nan yana gudana. Minista ba shi ne ya kirkiro yajin aikin ba, don haka ba shi da ikon dakatar da shi,” in ji Rilwan cikin wata hira da Daily Trust ta wayar tarho.

Yajin aikin wanda aka fara ranar Laraba, yajin gargaɗi ne na tsawon kwanaki bakwai da ƙungiyar ta NANNM ta fara a faɗin ƙasa. Ƙungiyar ta bayyana cewa yajin aikin ya samo asali ne daga matsalolin da suka haɗa da albashi, ƙarancin ma’aikata, bashin alawus, da kuma rashin ingantattun yanayin aiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here