Kungiyar Ma’aikatan Jinya Ta Dakatar da Yajin Aikinta

0
8

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta ƙasa (NANNM) ta dakatar da yajin aikin da take yi bayan wata ganawa da ta yi da Ministan Lafiya, Farfesa Ali Pate.

Tun da farko, kungiyar ta fara yajin aikin ne a matsayin gargaɗi na kwana bakwai daga ranar 29 ga Yuli, domin nuna rashin jin daɗinta game da matsalolin albashi, ƙarancin ma’aikata, da yanayin aiki.

A ranar Juma’a ne aka sanar da janye yajin aikin bayan wata ganawa tsakanin shugabannin kungiyar da Ministan a birnin tarayya Abuja.

Ko da yake ba a bayyana cikakken bayanin yarjejeniyar da aka cimma ba, dakatar da yajin aikin na nuna cewa an fara samun ci gaba wajen warware matsalolin da malaman jinya suka gabatar.

NANNM ta shiga yajin aikin ne don nuna ƙin amincewarta da yadda gwamnati ke tafiyar da batutuwan da suka shafi jin daɗin ma’aikata, yanayin aiki, da kuma tattaunawa da ƙungiyar. Sun bukaci karin alawus da kyautata yanayin aiki a cibiyoyin lafiya na tarayya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here