Kamfanonin Sadarwa Za Su Ci Gaba da Rajistar Sabbin Layi — Hukumar NIMC

0
12

Hukumar Kula da Shaidar Ƴan Kasa (NIMC) ta tabbatar da cewa kamfanonin sadarwa yanzu za su iya ci gaba da rajistar sabbin layukan waya, dawo da tsofaffi da kuma aiwatar da sauran ayyuka masu nasaba da layin waya wato SIM, ta hanyar tantancewa da lambar shaidar dan kasa (NIN).

Wannan ci gaba ya biyo bayan nasarar da aka samu wajen canja tsarin tantance NIN zuwa sabon dandali mai suna NINAuth, wanda hukumar NIMC ta ƙirƙira da kuma aiwatar dashi.

A cewar hukumar, NINAuth zai inganta tsaro, sauƙaƙa tantancewa, da kuma tabbatar da ingancin bayanan masu amfani da layin.

Haka kuma, dandalin zai bai wa hukumomi da kamfanoni damar samun sahihin bayani cikin aminci da tsari, domin tabbatar da asalin masu amfani da layukan waya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here