Gwamnatin Tarayya Za Ta Kashe Naira Biliyan 712 a Filin Jirgin Sama na Legas, Kano Kuma  Biliyan 46

0
5

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da kashe Naira biliyan 987 domin inganta muhimman ababen more rayuwa a wasu filayen jiragen saman ƙasar nan.

Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron Majalisar Zartaswar Tarayya (FEC) da aka gudanar a ranar Alhamis, ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu a Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa za a kashe Naira biliyan 712.26 wajen sabunta filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas, wanda aikin zai ɗauki tsawon watanni 22 kafin a kammala shi.

Kazalika, Majalisar ta amince da gyaran filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, akan Naira 46.39.

Ana sa ran aikin zai ƙare cikin makonni 24, tare da kuɗin da ya kai Naira biliyan 46.39, kuma zai taimaka wajen sauƙaƙa zirga-zirgar jirage musamman a lokacin hunturu, wanda ke janyo tsaiko da soke tashin jirage.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here