Yunwa ka’iya farfaɗo da rikicin Boko Haram–Majalsar Dinkin Duniya

0
14

Hukumar Shirin Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP) ta bayyana damuwarta kan yuwuwar jefa fiye da mutum miliyan ɗaya cikin haɗarin yunwa da kuma fuskantar barazanar ƙungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabas, sakamakon ƙarancin tallafin agaji.

WFP ta bayyana cewa ta ƙarar da kuɗaɗen da take amfani da su wajen tallafa wa waɗanda rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu, kuma hakan na barazana ga ci gaba da ayyukan jin ƙai a yankin.

Hukumar ta nuna fargaba cewa rashin tallafi na iya sanya wasu daga cikin waɗannan mutane su shiga hannun Boko Haram domin neman mafita.

A nasu ɓangare, ƙungiyar agaji ta likitoci ta MSF ta ce yunwa da rashin abinci mai gina jiki sun yi sanadin mutuwar yara fiye da 600 a yankin cikin wannan shekarar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here