Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Kiru/Bebeji a jihar Kano, Hon. Abdulmumini Jibrin Kofa, ya bayyana cewa ziyarar da ya kai wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a fadarsa na da nasaba da tattauna manyan batutuwan da suka shafi cigaban ƙasa.
A ranar Laraba ne Jibrin Kofa, wanda ke daga cikin fitattun jagororin jam’iyyar NNPP, ya gana da shugaban ƙasa a fadar da da ke Abuja, abin da ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin ‘yan Najeriya da dama musamman akan batun sauya sheƙar siyasa.
Sai dai yayin ganawa da manema labarai na fadar shugaban kasar, Jibrin Kofa ya ce babu abin mamaki a ziyarar, ganin kyakkyawar alaka da ke tsakanin shugaban ƙasa da kuma jagoran NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
“Ina ganin ba abin mamaki ba ne ganin tsohuwar alaƙar da ke tsakanin Shugaba Tinubu da Sanata Kwankwaso,” in ji shi.
Da aka tambaye shi ko wannan ziyara na da nasaba da yiwuwar komawar Sanata Kwankwaso zuwa jam’iyyar APC, Jibrin Kofa ya ce: “Ba lokacin wannan maganar bane yanzu, amma komai na iya faruwa.”
Ya ƙara da cewa, “Lokaci zai bayyana komai, kuma kowa zai sani.”