Kudin Da Aka Bawa Super Falcons Na Iya Biyan Albashin Likitoci 16,000, Malamai 66,000 Da ‘Yan Sanda Masu Ƙananan Matsayi 78,000 — Daily Trust

0
14

Wani Rahoton Jaridar Daily Trust ya bayyana cewa kudin da aka bai wa ƴan wasan Super Falcons bayan nasarar da suka samu a gasar WAFCON 2024 ya kai Naira biliyan 4.952, kuma wannan adadi na iya biyan albashin ma’aikata masu muhimmanci kamar likitoci 16,000, malamai 66,000, da ‘yan sanda ƙanana fiye da 78,000 na wata guda.

Ƴan wasa 24 sun samu kyautar $100,000 kowanne, yayin da jami’an gudanarwar tawagar su 11 suka samu $50,000 kowanne. Haka kuma, Shugaba Bola Tinubu ya ba su lambobin girma da gidaje.

Sai dai wannan karramawa ta haifar da cece-kuce, inda mutane da dama ke ganin cewa za a iya amfani da irin wannan kuɗi wajen inganta fannin lafiya, ilimi da tsaro, maimakon kashewa ƴan wasa kawai.

Wani mai sharhi, Fr. Kelvin Ugwu, ya ce jimillar kudin da aka kashe don murnar lashe kofin da darajarsa ke $1m, ya haura $5m, ciki har da kyaututtuka, gidaje da bikin tarbar su, wanda ya bayyana a matsayin rashin fifita bukatun al’umma a lokacin da tattalin arziki ke ƙara tabarbarewa.

Rahoton ya kuma bayyana cewa ƙalubalen da likitoci da malamai ke fuskanta na rashin albashi mai kyau da yanayin aiki mara kyau, shi yada da dama ke barin ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here