Wata babbar kotu a jihar Kwara ta yanke hukuncin kisa ga wani da aka ayya a matsayin malami mai suna, Abdulrahman Mohad, bisa samunsa da laifin kisan gilla da aka yi wa Hafsoh Lawal Yetunde, wadda ta kasance daliba ‘yar aji na ƙarshe a Kwalejin Ilimi ta Jihar Kwara.
Mai shari’a Hannah Ajayi ce ta yanke hukuncin a ranar Alhamis, inda ta tabbatar da cewa Mohad ya kashe dalibar ne domin yin tsafin kudi.
Sai dai kotun ta wanke wasu mutane hudu da ake zargi sunyi kisan tare da shi, su ne Ahmed Abulwasiu, Sulaiman Muhydeen, Jamiu Uthman, da AbdulRahman Jamiu, bisa rashin shaida da za ta tabbatar da hannunsu a cikin lamarin.
Lamarin ya faru ne a ranar 10 ga Fabrairu, 2025, lokacin da Hafsoh ta bace bayan ta amsa wani kiran waya yayin da take halartar bikin sunan jariri. Bacewarta ta tayar da hankali, wanda hakan ya sa ‘yan sanda suka fara bincike. Binciken ya kai ga cafke Mohad da sauran mutum hudu, bayan an bi sahun wayarta.
A cewar rahoton farko na ‘yan sanda, wadanda ake zargin sun amsa laifi tun farko, inda suka bayyana cewa suna cikin wata ƙungiyar asiri kuma sun janyo Hafsoh ne don su yi amfani da ita wajen tsafi. Amma daga baya, Mohad ya fitar da faifan bidiyo inda ya ɗauki dukkan laifin a kansa, yana mai cewa sauran ba su da hannu a cikin lamarin.
Kotun ta dogara da shaidun da aka gabatar da kuma amsar laifi da Mohad ya yi don yanke masa hukuncin kisa, yayin da sauran suka sami ‘yanci.