Jam’iyyar PDP a Kano ta nesanta kanta daga haɗakar ADC

0
19

Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kano, Hon. Yusuf Ado Kibiya, ya bayyana cewa basu da wata alaƙa da wani rukuni da ke nuna goyon baya ga jam’iyyar ADC, yana mai cewa irin wadannan mutane basa wakiltar jam’iyyar PDP a Kano.

A wata ganawa da manema labarai da ya yi a ranar Alhamis, Kibiya ya bukaci mambobin jam’iyyar da su ci gaba da dagewa tare da gujewa rudani da masu ƙoƙarin yaudarar al’umma.

Ya kuma bayyana wasu nasarorin da PDP ta cimma kwanan nan, ciki har da kammala tarukan zabukan matakai na gunduma, ƙananan hukumomi, da na jiha. Ya ce waɗannan nasarori alamu ne na ƙarfin tsarin cikin gida na jam’iyyar da kuma jajircewarta ga tsarin dimokuraɗiyya.

Kibiya ya ƙara da cewa an rantsar da dukkan shugabannin jam’iyyar da aka zaɓa a matakai daban-daban, kuma yanzu sun shirya tsaf wajen aiwatar da manufofi da ayyukan jam’iyyar. 

Ya jaddada biyayya da amincewar jam’iyyar PDP ta Kano ga shugabancin ƙasa na jam’iyyar, tare da tabbatar da cewa su na bin umarnin jam’iyyar a matakin ƙasa da ƙarfafa haɗin kai.

Kibiya ya kuma tabbatar wa da al’umma cewa PDP a Kano na tafiya da cikakken haɗin kai tare da niyyar gina jam’iyya mai ƙarfi domin fuskantar zaɓuɓɓuka masu zuwa, da kuma samar da shugabanci na gari wanda zai magance buƙatun talakawa.

A ƙarshe, ya buƙaci al’ummar Kano da su yi rijista da PDP, yana mai bayyana jam’iyyar a matsayin ingantacciyar hanyar kawo cigaba a matakin jiha da ƙasa baki ɗaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here